• Labaran yau

  July 25, 2017

  Saurayi ya kasheta domin tana soyayya da Musulmi

  Celine Dookhran 'yar shekara 19 kuma 'yar asalin kasar Indiya Musulma,ta gamu da ajalinta ne sakamakon soyayya da ta fara da wani balarabe Musulmi lamarin da bai yi wa wasu samari 'yan asalin kasar India dadi ba.

  Rahotanni sun nuna cewa maharan sunkai wa Celine farmaki ne a gidan da take ciki a Wemblin suka kamata suka daureta bayan sun toshe masu baki da tsumma ita da kawarta wanda suke a daki daya.

  Maharan sanye da hula da ya rufe fuskokinsu sun dunkule kawayen biyu a bargo suka tafi da su wani gida da ba a kammala ba a yammacin London inda aka yi wa Ciline fyade kana aka kasheta ta hanyar yankan rago.

  Haka ya kasance da kawarta wanda daga bisani ta samu tserewa kuma ta shaida wa 'yansanda daga gadonta na Asibiti.

  Mujahid Arshid dan shekara 33 da Vincent Tappu sun bayyana a gaban Kotu a bisa tuhumarsu da aikata laifin da ya kai ga kisan Celine da yunkurin kashe kawarta.  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saurayi ya kasheta domin tana soyayya da Musulmi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama