Rashin biyan albashi - Ma'aikacin Gwamnati ya zama mai tallar gyada

Mr Godwin Ogar dan shekara 46 ma'aikaci ne a ma'aikatar tsabtace birni na jihar Benue wanda ya fara sayar da gyada sakamakon rashin biyan albashi na wasu watanni wanda Gwamnatin jihar Benue batayi ba.

Lamarin mai ban dariya da tausayi ne,kamar Mr.Godwin yana tallar gyada kuma babu girman kai ko kunya cewa ai ma'aikacin Gwamnati yanzu kuma yana tallar gyada.

Godwin mahaifin yara uku ne,ya ce ya kasa samarwa yaransa abinci ne don rashin kudade da zai tafiyar da lamurran gidansa shi yasa ya yanke shawarar cewa ya fara sayar da gyada domin ya sami kudinda zai ciyar da iyalinsa.

Ya kara da cewa gomma ya yi tallar gyada bisa yaje yayi sata ko ya wulakanta kansa wajen maida kansa mabaraci da gangan.


Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga shafinmu kai tsaye www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Rashin biyan albashi - Ma'aikacin Gwamnati ya zama mai tallar gyada Rashin biyan albashi - Ma'aikacin Gwamnati ya zama mai tallar gyada Reviewed by on July 19, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.