• Labaran yau

  July 31, 2017

  Osinbajo zai buda kamfanin sarrafa shinkafa WACOT a Argungu

  Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai ziyarci jihar Kebbi ranar Talata 1 ga watan Agusta ziyarar da zata kaishi ga buda katafaren kamfanin sarrafa shinkafa WACOT a garin Argungu.

  An kiyasta cewa kamfanin zai samar wa akalla mutum 1000 aiki ta la'akari da cewa kashi 95 a cikin ma'aikatan zasu kasance 'yan  asalin jihar Kebbi.

  Lissafi ya nuna cewa an kashe akalla naira biliyan goma N10b wajen girka kamfanin da ake zaton zai iya samar da ton 400 na shinkafa a kowane rana.

  Hakazalika Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu a wata sanarwa da ta fito daga hannun sakataren watsa labarai na Gwamnan Abubakar Mu'azu Dakingari ya bukaci jama'ar jihar Kebbi su fito kwansu da kwarkwatansu domin su tarbi mataimakin shugaban kasa a jihar Kebbi.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Osinbajo zai buda kamfanin sarrafa shinkafa WACOT a Argungu Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama