• Labaran yau

  July 04, 2017

  Mutum 4 sun mutu yayin musanyar wuta tsakanin soji da yan fashi | isyaku.com

  Mutum hudu sun mutu a yayin da ake musanyar muta tsakanin wasu 'yan fashi da makami da kuma wasu jami'an sojin Najeriya da suka yi kokarin dakile fashin a unguwar Ajah da ke garin Lagos da yammacin yau.

  Lamarin ya rutsa da mutum hudu fararen hula cikin su har da wata mata wanda albarushi ya same su sakamakon barin wuta da ya gudana tsakanain 'yan fashin da sojoji.

  Wadanda lamarin ya rutsa da su fasinjoji ne da ke cikin wata karamar motar haya.

  Bayanai sun nuna cewa biyu daga cikin 'yan  fashin sun halaka sakamakon musanyar mutar tsakaninsu da sojoji.

  Babu wani karin bayani akan ko akwai cikin jamai'an soji da ya jikata a cikin lamarin.


  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 4 sun mutu yayin musanyar wuta tsakanin soji da yan fashi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama