Mutum 16 sun kone kurmus sakamakon hatsarin mota

Akalla mutum 16 ne suka mutu kurmus sakamakon wani mummunar hatsarin mota da ya rutsa da su,motar mai daukan mutum 18 kirar Toyota Hiase tayi karo ne da wata tankar jigilar man fetur bayan motar ta kwace ma direban nan take hakan ya haddasa mumunar gobara da ta lakume ilahirin motocin a ranar Lahadi 23/7/2017.

Lamarin ya faru ne a garin Ille-Ife na jihar Ondo yayin da kofofi na motar bus din mai lamba (LAGOS) MUS 702 XH suka ki budewa balle a taimaki fasanjojin da ke makale a cikinta yayin da wutar ke ci.

An yi amfani da gatari aka sassare motar kafin a fiddo mamatan wanda suka hada da kananan yara guda biyu..
Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Mutum 16 sun kone kurmus sakamakon hatsarin mota Mutum 16  sun kone kurmus sakamakon hatsarin mota Reviewed by on July 24, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.