• Labaran yau

  July 14, 2017

  Mugunta ko keta-An kone gonar wani Dattijo da feshin magani

  Kamar yadda kuka gani wannan gonar wani bawan Allah ne mai suna Mal.Bala mutumin Hori-gari , wani Kauye ne da ke cikin karamar hukumar Mulki ta Shanga a jihar Kebbi. Shi dai malam Bala an wayi gari yazo gonarsa kawai sai ya taradda wannan aika-aikan , wato wani mutun wanda baisan ko waye ba yazo ya feshe mai gona da maganin feshi wanda kusan rabin gonar ya kama hanyar halaka !
  Shidai wannan gonar yana nan kudu maso yamma daga Makarantar kimiya da fasaha da ke cikin garin Saminaka wato" GSTC" .
  Ni kaina da naga wannan aikin wallahi Saida hankalina ya tashi sosai ! Domin ko baka son wannan dattijon matukar kaga wannan aiki dolene kaji tausayinsa.

  Idan Manomi zai iya karar MAKIYAYI saboda anci mashi abinda baikai kuyya dayaba , to wannan aikin da akayi a wannan gonar  yafi dacewa ace anyi kara/hayaniya saboda shi .
  Amma abinda zai baka mamaki , na tambayi wannan dattijon Mal. Bala ko yasan wanda yayi wannan aikin ?
  sai yace tabbas akwai wanda ya ke tuhuma akai !
  Nace to shi wanda kake tuhumar yazo wurin ka domin nuna kuskurensa da neman yafiyarka akan wannan ?
  Yace A'a !
  Nace to kai akwai wani mataki da ka dauka/zaka dauka akansa ?
  Yace A'a , shidai kawai yana jiransa idan yazo zai saurareshi idan bai zo ba ba wani mataki da zai dauka akansa saidai kawai su hadu dashi gobe gaban Allah . Allah Sarki , irin Wannan "Lafazin" akwai hadari gareshi sosai idan yana fitowa daga bakin Dattijawa .
  musamman idan ka tsokanesu .

  Daga Sani Musa Saminaka.

  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mugunta ko keta-An kone gonar wani Dattijo da feshin magani Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama