• Labaran yau

  July 12, 2017

  Matsafa sun gundule kan 'yan uwan juna da mutum 3 a jihar Rivers | isyaku.com

  Harkar matsafa da kungiyoyin asiri ya fara zama annoba a jihar Rivers inda 'yan wadannan kungiyoyin suke cin karensu ba babbaka.An wayi garin an ga gawaki biyar a sassa daban daban a jihar ta Rivers ciki harda gawakin wasu da aka shaida cewa 'yan uwan juna ne wa da kanensa.

  Bayanai sun nuna cewa wasu yan kungiyar asiri ne suka shigo garin Umudioga ranar Litinin da dare a karamar hukumar Ikwerre kuma suka kashe wadannan yara matasa 'yan uwan juna da sauran jama'a ta hanyar gundule kawunan su.

  'Yan uwan juna da aka gundule kawunansu an shaida cewa Emeka da Ifeanyi Wobo ne haifaffun garin Rumuokpareli, a cikin al'umman Obio/Akpo.Wasu karin gawakin kuwa an tsince su ne a wasu sassa ciki harda wata gawa da aka tsinta a kan hanyar NTA a birnin Port Harcourt wanda ba'a gane ko waye ba.
  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matsafa sun gundule kan 'yan uwan juna da mutum 3 a jihar Rivers | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama