• Labaran yau

  July 11, 2017

  Matashi ya tube zindir yayi dambe da Dansanda a Lagos | isyaku.com

  Wani Matashi ya tube zindir kuma yayi dambe da wani jami'in 'dan sanda a unguwar Ikorodu da ke jihar Lagos.

  Wani hoton bidiyon mai tsawon minti daya ya nuna yadda matashin ya tube zindir yana fada da wani dansanda wanda  motarsu ke tsaye a kan titi.

  Matashin da yake tsirara ya yi nassarar maka dansandan da kasa kuma ya rike shi daram a yayin da dansandan yayi kokarin komawa cikin motarsu saboda ya bar wajen amma matashin ya rike shi daram.

  Irin wannan abun kunya na kin karawa yakan faru ne kawai a nahiyar Africa musamman kudancin Najeriya.

  Idan baku manta ba haka wani Malami a 'yan kwanakin nan a garin Baham da ke arewacin kasar Cameroun ya tube wasu dalibai mata 'yan Makaranta zindir kuma yabi su ya bulale su a duwawu wai saboda sun yi latti wajen zuwa Makaranta.  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matashi ya tube zindir yayi dambe da Dansanda a Lagos | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama