• Labaran yau

  July 26, 2017

  Matar aure mai shekara 14 ta kashe mijinta da tabarya

  Hukumar 'yansanda a jihar Niger ta kama wata matar aure mai shekara 14 mai suna Aisha Isah wadda ake zargi da kashe mijinta Isiaka Usman dan shekara 40 a kauyen Lifari da ke cikin karamar hukumar Mashegu.

  Bayanai sun nuna cewa Aisha da maigidanta marigayi Isiaka 'yan uwan juna ne diyan wa da kane.Bayan an daura aure tsakanin su wadda dama Isiaka yana da mata biyu Aisha ce matarsa ta uku.

  Daga bisani Aisha ta yi ta koke akan  cewa baya ciyar da ita,Rahotanni sun nuna cewa a bisa irin wannan zargi na rashin ciyarwa ne dayan matar tashi  ta fice daga gidansa.

  A cewar Aisha,wata rana ta fuskance shi ne da zancen rashin ciyarwa har kwana biyu,bayanin da ya zama sanadin rigima a tsakaninsu da ya kaita ga daukan tabarya ta kwantara masa a kai wanda nan take ya yanke jiki ya fadi.

  An garzaya da Isiaka Asibiti zuwa Asibitin Mashegu Hospita inda yayi takaitaccen jinya daga bisani rai yayi halinsa.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Niger Bala Elkana ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce za'a kai Aisha Kotun wadanda basu cika shakara 18 ba (juvenile court) domin ta fuskanci hukunci.


   

  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matar aure mai shekara 14 ta kashe mijinta da tabarya Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama