• Labaran yau

  July 24, 2017

  Maniyyata 6.000 ne zasu je aikin Hajji a jihar Kaduna

  Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Kaduna tace zata fara aikin jigilar Alhazan jihar daga ranar 1 ga watan Agusta.

  Mai magana da yawun hukumar Alhazan Malam Yunusa Abdullahi ya shaida wa majiyarmu cewa an kammala takardun Visa na maniyyata 5000 kuma ana daf da kare aikin Visan ragowan maniyyatan.

  Mal.Abdullahi yace mutum 6.247 ne suka biya kudin Hajjin bana akan Naira Miliyan 1.53 akan kowane Maniyyaci.

  Ya kara da cewa Maniyyatan da basu kammala biyan kudadensu ba su hanzarta biya kafin ranar Juma'a 28/7/2017.




  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Maniyyata 6.000 ne zasu je aikin Hajji a jihar Kaduna Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama