Majalisan Dattawa ta rage karfin ikon Shugaban Kasa

Majalisan Dattijai na Najeriya ta kada kuri'a da gagarumin rinjayen inda ta amince da yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Dattawan sun amince da yin kwaskwarima ga 29 cikin kudirori 33 da aka gabatar a gabanta domin dubawa.

Haka zalika Majalisar ta rage karfin ikon shugaban kasa akan ababen da suka shafi ikon Majalisan Dokoki ta Najeriya.

An sami kuri'u 92 yayin da 4 suka ki amincewa da kudirin da ya rage ikon shugaban kasa wajan yin gaban kanshi domin yaki amincewa da kudurin Majalisa.

Kudurin har ila yau ya aminta da ganin cewa tsofaffin shugabannin Majalisan Dattijai da na Wakilai zasu kasance a cikin jerin majalisar zartarwa na jihohi.

Kudurin ya samar da dokar kariya ga 'yan Majalisan Dattawa da na Wakilai na tarayya da na jihohi akan kalamai da suka yi ko suka rubuta a wajen muhawwara ko gabatar da wani kuduri a kwamiti.

Haka kuma dokar zata tilasta shugaban kasa ya bayyana a kalla sau daya a gaban Majalisa a lokacin babban taronta.

Dole kuma shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudi a gaban Majalisa kwana 90 kafin karewan shekaran da ake ciki.Haka zalika Gwamnonin jihohi.




Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN