• Labaran yau

  July 05, 2017

  Kotu: A fitar da sunayen barayin dukiyar Najeriya | isyaku.com

  Wata Alkalin wani babban Kotun tarayya da ke jihar Lagos Justice Hadiza Rabiu Shagari ta baiwa Gwamn
  atin tarayyar Najeriya umarnin cewa ta fitar da sunayen manyan jami'an gwamnati da ita Gwamnatin tace ta karbo kudaden al-mundahhana daga wajen su daga watan Mayu 2015 zuwa Mayu 2016.

  Justice Shagari ta fadi haka ne a yayin da take yanke hukunci akan karar da wata kungiyar kare hakkin fararen hula ta SERAP ta shigar a gaban Kotu inda ta bukaci Gwamnatin tarayya ta gaya wa 'yan Najeriya sunayen jami'an Gwamnati da abin ya shafa ko ta gurfanar da Gwamnati a gaban Kotu cikin wa'adin kwanaki 14.

  Gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwa ta hannun Ministan watsa labarai Lai Muhammed cewa Gwamnati ta karbo kudaden al'mundahhana da wasu manyan jami'an Gwamnati suka wawure wanda adadin ya kai har kusan  N78,325,354,631.82, $185,119,584.61, £3,508,355.46 da €11, 250 da Mayu 29th 2015 to Mayu 25th 2016. 

  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu: A fitar da sunayen barayin dukiyar Najeriya | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama