Kotu ta daure yan fashi shekara 150 a gidan yari

A yankin Ashiman a kasar Ghana wata Kotu ta yanke wa wasu samari da aka samu da laifin aikata fashi da makami hukuncin daurin shekara 150 a gida yari.

Wadanda aka daure sun hada da Rashid Nurudin wanda aka fi sani da suna Torgbor, 20, wani mai aikin feshi; Prince Tetteh Agormeda, 18, dan acaba; Saviour Feda, 21, yaron mota; Kelvin Baah,19, wani dan jigila da Francis Kwasi,19, yaron mota.

Alkali  Gabriel Mate-Teye ya banka masu daurin shekara 30 kowannensu bayan ya same su da laifin aikata fashi da makami a garin Zenu na gundumar Kpone-Katamansu a kasar ta Ghana.

An kama matasan ne da laifin shiga wani gida ta kofar baya inda suka saci talabijin na bango,wayar salula da sauran kayaki bayan samarin su biyar sun yi wa mai gidan barazana da makamai da misalin karfe 1:30 na dare a bara.Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Kotu ta daure yan fashi shekara 150 a gidan yari Kotu ta daure yan fashi shekara 150 a gidan yari Reviewed by on July 23, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.