• Labaran yau

  July 29, 2017

  Kotu ta daure basaraken gargajiya shekara 1 a gidan yari a bisa laifin damfara

  Wata babban Kotu a jihar Kano karkashin Alkalancin Mai shari'a Nasiru Saminu ta daure wani basaraken gargajiya Umar Kabir Danbaba shekara daya a gidan yari bayan ta same shi da laifin cin amana.

  Hukumar kula da masu yi ma tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC ta gabatar da basaraken a gaban Kotu bayan wani koke da ta samu game da shi inda ya damfari mai koken zunzurutun kudi har Naira Miliyan daya da dubu dari hudu da saba'in (N1,470,000).

  Mai karan ya baiwa Umar kukaden ne domin ya sama masa wuri da tsari  da zai tafiyar da harkar ginan ma'adanai amma sai ya damfareshi.  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta daure basaraken gargajiya shekara 1 a gidan yari a bisa laifin damfara Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama