• Labaran yau

  July 01, 2017

  Kontagora:Tashin hankali tsakanin matasa da 'yan banga yayi sanadin mutuwar mutum 2 | isyaku.com

  An sami tashin tashina sakamakon mutuwar wani matashi dan shekara 17 a hannun kungiyar banga ta Vigilante da ke unguwar Yaman a karamar hukumar Kontagora na jihar Niger a ranar Alhamis da ya gabata.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Niger DSP Bala Elkana ya tabbatar da haka wa manema labarai.

  Elkana ya kara da cewa mutum biyu ne suka mutu yayinda wasu mutum biyar suka sami munanan raunakka ciki har da wata budurwa da ta ke cikin mumunar yanayi sakamakon raunin da ke a jikinta.

  Bayanai sun nuna cewa mutum na biyu dan shekara 20 ya mutu ne sakamakon harbi da bindiga da 'yan bangan suka yi a yayin da masu zangazangar suka yi kokarin kona ofishin 'yan bangan.

  Hukumomi a jihar ta Niger sun tura 'yansandan kwantar da tarzoma domin shawo kan lamarin.Yayin da yansanda suka kama 'yan bangan na Vigilante su biyu da ake zargi da azabtar da matashin da hakan yayi sanadin mutuwarsa.  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kontagora:Tashin hankali tsakanin matasa da 'yan banga yayi sanadin mutuwar mutum 2 | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama