Kebbi ta shirya tarbar mataimakin shugaban kasa - Dododo ya roki jama'a su nuna dattaku

Yayin da mahukunta a jihar Kebbi suka shirya tsap domin karban bakoncin ziyarar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ziyara da ake kyautata zaton zai kawo a jihar Kebbi ranar Litinin 1 ga watan Agusta wasu jama'ar jihar ta Kebbi suna dakon ganin ko wane alhairine wannan ziyarar zai iya haifarwa.

An shirya buda wani katafaren Kamfanin sarrafa shinkafa wanda ba mallakan Gwamnati bane a garin Argungu wanda aka kiyasta ya ci kudi zunzurutu har Naira biliyan 10 wanda mataimakin shugaban kasa zai bude da kanshi.

An tsabtace manyan titunan garin Birnin kebbi musamman hayoyi da ake zaton mataimakin shugaban zai bi.

A wani jawabi da yayi da mu ta wayar salula,mai magana da yawun jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh.Sani Dododo ya bukaci jama'ar jihar Kebbi su nuna mutunci da dattaku ga tawagar mataimakin shugaban kasa,musamman tawagar da ke fara isowa kafin mataimakin shugaban ya iso.

Alh.Sani ya kara da cewa jama'ar jihar Kebbi an san su da dattaku saboda haka ya roki jama'a su nuna dattaku ga tawagar kuma su fito kwansu  da kwarkwatan su domin su karrama mataimakin shugan kasa wajen tarbon shi a jihar ta Kebbi.Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Kebbi ta shirya tarbar mataimakin shugaban kasa - Dododo ya roki jama'a su nuna dattaku Kebbi ta shirya tarbar mataimakin shugaban kasa - Dododo ya roki jama'a su nuna dattaku Reviewed by on July 30, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.