• Labaran yau

  July 13, 2017

  Kebbi: Jami'an FIRS suna zagayawa don ilmantar da masu sana'oi tsarin biyan haraji

  Jami'an hukumar tattara haraji na cikin gida ta kasa FIRS sun fara zagayawa cikin garin Birnin kebbi domin sanar da masu  shaguna da kananan sana'oi tsarin biyan haraji wanda ya kunshi nau'i daban daban a bisa tsari jaddawalin haraji da ya shafi irin sana'ar da mutum ke yi.

  Mr. Ibrahim Mahe Yakubu ya shaida wa ISYAKU.COM cewa suna gudanar da wannan aikin ne domin ilmantarwa ,sanarwa da kuma fadakar da masu shaguna da sana'oi akan tsarin da ya shafe su wajen biyan haraji da ya jibanci FIRS.

  Mr Ibrahin ya shaida mana cewa "ana bukatar wannan haraji ne saboda inganta rayuwar 'yan Najeriya musamman domin a rage dogaro da man fetur wajen samun kudin shiga a Najeriya".

  Jami'an hukumar sun fito kwansu da kwarkwatansu inda aka gansu suna zagayawa shago shago a Ahmadu Bello way  da wasu tituna da ke cikin garin Birnin kebbi.
  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Jami'an FIRS suna zagayawa don ilmantar da masu sana'oi tsarin biyan haraji Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama