• Labaran yau

  July 28, 2017

  Kebbi - Gwamna Atiku ya yaba wa zaben Mata 19 a matsayin Kansila

  Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya yaba wa zaben da akayi wa Mata 19 a matsayin Kansila a zaben kananan hukumomi da aka kammala a jihar a makon da ya gabata.

  Haka zalika Gwamnan ya gode wa jama'ar jihar Kebbi da suka fito kwansu da kwarkwatansu suka zabi jam'iyar APC.

  Ya kuma kara da godiya akan yadda jama'a suka yi amanna da Gwamnatinsa.

  Gwamna Atiku ya ce Gwamnatinsa tana bayar da kulawa ga harkokin mata kamar yadda ya kamata tun daga lokacin da ya kama mulkin jihar kuma zai ci gaba da ba Mata da jama'an jihar Kebbi ingantaccen kulawa.


  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi - Gwamna Atiku ya yaba wa zaben Mata 19 a matsayin Kansila Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama