• Labaran yau

  July 29, 2017

  Jami'ar Maiduguri ta caccaki sojin Najeriya

  Shugaban Jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya, Abubakar Njodi ya caccaki rundunar sojin kasar bisa ikirarinta na ceto ma’aikatan hakar man fetir da mayakan Boko Haram suka yi wa kwanton- bauna.
  Njodi ya ce, har yanzu ya gaza fahimtar dalilin da ke sa rundunar sojin Najeriya ke yada labaran jabu.
  Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojin ta ce, ta ceto dukkanin manazarta kimiyyar kasa na jami’ar Maiduguri da ke aiki da kamfanin mai na NNPC.

  A cewar Njodi, jami’ar ta Maiduguri ta yi rashin zaratan malamai hudu a sashen kimiyyar kasa sakamakon farmakin na Boko Haram, kuma ya ce, babu wanda ya yi kasa da shekara 10 a cikinsu yana karantawar, abin da ya bayyana da babbar asara ga jami’ar.

  "Mawuyaci ne a gare ni na samu wadanda za su maye guraben wadannan malamai da muka yi rashinsu." in ji shugaban Jami'ar.

  Njodi ya bayyana cewa, gano gawarwakin da sojin suka yi, ba ya nufin ceto manazartan.

  Boko Haram ta dirar wa tawagar masana kimiyar kasar ne da wasu jami’an tsaro akan hanyarsu ta zuwa aikin gano man fetir a karkashin jagorancin kamfanin NNPC a yankin tafkin chadi.

  Wasu rahotanni na cewa, kimanin mutane 40 ne suka mutu da suka hada da jami'an tsaro a dalilin farmakin.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

  Daga RFI
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jami'ar Maiduguri ta caccaki sojin Najeriya Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama