• Labaran yau

  July 26, 2017

  Jami'an tsaro sun tube 'yar kunar bakin wake

  Jami'an tsaro sun kama wata budurwa 'yar kunar bakin wake da ta yi damara da rigar bamabamai a yayin da take kokarin satan shiga kauyen Kawuri a karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

  Jami'an tsaron sun tubeta har zuwa bante saboda su tantance cewa lallai babu wani abu mai lahani a jikinta.

  Wani dan sintiri daga cikin jami'an tsaron ne ya gano ta yayin da take lalabe domin ta saci jiki ta shiga Kuwari inda take son ta tayar da bamabaman.  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jami'an tsaro sun tube 'yar kunar bakin wake Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama