• Labaran yau

  July 18, 2017

  "Ina son in kware wajen magana da harshen Turanci" - Adam A. Zango

  Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya ce babban burinsa shi ne ya kware wajen magana da harshen Turanci.

  Zango, wanda aka haifa a garin Zangon Kataf na jihar Kaduna, ya yi karatun sakandare a birnin Jos na jihar Plateau ne.Jarumin a yanzu dai haka ya dauki malamin da yake ba shi darussa a gida, kafin ya koma makaranta don cigaba da karatun.

  A wani hira da yayi da BBC Jarumin ya ce zai bar sana'arsa nan da dan wani lokaci domin ya je ya ci gaba da karatun boko.Sai dai wani abu da Adam ya ce yana ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu ‘yan boko suke masa kallon jahili duk kuwa da cewa “na yi karatun bokon sannan kuma ina da ilimin addini.”  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://www.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: "Ina son in kware wajen magana da harshen Turanci" - Adam A. Zango Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama