• Labaran yau

  July 26, 2017

  Gini mai hawa 4 ya ruguje,mutum 8 sun mutu an ceto mutum 15

  Hankalin jama'a ya tashi matukar gaske a unguwar Massey da ke birnin Lagos yayin da wani gini mai hawa 4 ya ruguje da tsakar rana misalin karfe 2:00 ranar Talata.

  Kawo yanzu bayanai sun nuna cewa mutum 8 ne suka mutu yayin da 15 suka sami raunukka.

  Jami'an hukumar bayar da taimako na gaggawa na jihar Lagos LESAMA suna kokarin taimakawa ko da za'a ceto karin wasu da rai bayan an ceto wani yaro mai shekara 11 jiya da yamma misalin karfe 4:00.

  Premium Times ta ruwaito cewa janar manaja na LESAMA Mr.Adesina Tiamiyu ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace an ceto yaro mai shekara 11 da ransa yayin da mutum 15 suka sami raunukka.  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gini mai hawa 4 ya ruguje,mutum 8 sun mutu an ceto mutum 15 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama