• Labaran yau

  July 25, 2017

  Boko Haram ta kashe Kwamandan Maharban Adamawa Bukar Jimeta

  Rahotanni sun nuna cewa mayakan boko haram sun kashe shugaban kungiyar maharba na jihar Adamawa Bukar Jimeta bayan wani artabu tsakanin 'yan kungiyar boko haram da maharban wanda daga karshe yayi sanadiyar mutuwar Kwamanda Bukar.

  Muryar Amurka ta ruwaito cewa Kwamanda Jimeta ya rasa ransa ne bayan da suka kai dauki a garin na Dagu wanda Boko Haram ta kai wa hari.

  Har ila yau harin ya yi sanadin mutuwar wasu maharba uku, amma bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan Boko Haram su ma sun rasa mayakansu da dama.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Boko Haram ta kashe Kwamandan Maharban Adamawa Bukar Jimeta Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama