• Labaran yau

  July 12, 2017

  Baturiya ta tofa wa Musulma yawu domin ta sa Hijabi | isyaku.com

  A wani abin da za'a iya kira kin jinin Musulmi da Musulunci wata mata mai suna Nnox Mulder ta tofa wa wata yarinya mai suna Wasi yawu a fuska wai kawai saboda Wasi Musulma ce da take sanye da Hijabi.

  Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru a tsakiyar birnin London yayin da Wasi da abokinta ke tattakawa kwasam sai Nnox wadda farar fata ce ta nufatosu kuma nan take ta tofa wa Wasi yawu a fuska.

  Abokin Wasi watau Rahman ya dauki hoton farar fatar da ta tofa wa Wasi yawu kuma ya sanya a shafukan sada zumunta da niyyar cewa sakon ya zagaya al'umma domin mutane su kiyaye kuma su yi hattara da
  Knox yar kyamar Musulunci da Musulmai ce.


  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Baturiya ta tofa wa Musulma yawu domin ta sa Hijabi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama