Ana gudanar da zaben kananan Hukumomi da Kansila a jihar Kebbi

Da safiyar yau Asabar a dukkanin kananan hukumomi 21 da babban Birnin jihar Kebbi garin Birnin kebbi jama'a na ta fitowa suna kada kuri'un su don zaben shugabanin kananan hukumomi da Kansilolin su a zaben da hukumar 'yansanda ta jihar tace zata samar da jami'anta guda 5000 domin su bayar da tsaro a lokacin zaben a fadin jihar.

Kamar yadda aka saba a bisa al'adar gudunar da zabuka a Najeriya,dukkannin runfunan zabe da ISYAKU.COM ya ziyarta ma'aikan zabe da jami'an tsaro suna kan aikinsu,wanda a halin yanzu yake tafiya ba tare da wani tangarda ba. 

Saidai kusan rinjayen runfunan zabe da muka ziyarta a garin Birnin kebbi akwai wakilan jam'iyyu musamman APC,AP da PDM amma babu wakilai na PDP watau agent.

Kokarin mu na muji ta bakin mai magana da yawun jam'iyar PDP na jihar Kebbi yaci tura har izuwa lokacin da muka rubuta wannan labari.

Wata majiya ta shaida mana cewa kauracewar jam'iyar PDP bazai rasa nasaba da karin kudin fom na 'yan takara ba wanda tun farko bayanai sun nuna cewa 'ya'yan jam'iyar ta PDP sun koka akan tsadar fom din wanda dan takaran Kansila zai biya N200.000 sabanin yadda yake a da na N50.000 da kuma dan takaran shugaban karamar hukuma Ciyaman N500.000 sabanin N200.000 a can baya.

Amma Alh.Sani Dododo Mai magana da yawun jam'iyar APC na jihar Kebbi ya shaida mana ta wayar tarho cewa "Idan ma akwai kaurace wa rumfunan zabe da agent na wata jam'iya ta yi wannan bai shafesu ba kuma hakan ba zai taba zama barazana a garesu ba."

"A jaddawali da lokaci da hukumar zabe ta tsara kumar ta shirya akan wannan zabe,ba a hana kowace jam'iya cika hakkinta ba ko aka tauye wata jam'iya ba.Hukumar zabe ta gudanar da komi akan tsari kuma ake tafiyar da komi akan tsarin mulki da ka'idodin hukumar zabe.Idan agent na wata jam'iya basu zo rumfunan zabe ba ai kamar sun raina ko sun cuci jam'iyarsu ne ba kowaba"


Daga  Isyaku Garba - Birnin kebbi




Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN