• Labaran yau

  July 10, 2017

  An tsinci gawar wata mace a kan gada a jihar Delta | isyaku.com

  An tsinci gawar wata matashiya mace a kan gadar Otokutu a babban titin DSC a karamar hukumar Ughelli a jihar Delta.

  Rahotanni sun nuna cewa har izuwa yanzu ba'a gane ko wace ba.

  Mazauna wannan unguwa na rade radi da zargin cewa watakila an kashe ta ne aka jefar da ita a gadan.

  Yanzu haka hukumomi a jihar ta Delta sun dukufa domin gano 'yan uwa da iyalan mamaciyar tare da gano musabbabin mutuwarta.

  Hotuna sun bayyana a shafin sada zumunta na Facebook inda wani mai suna Christian Onwugbolu ga abinda ya wallafa a shafin nasa:

  An samu labarin cewa an jefar da gawar wannan matan ne bayan an kashe ta an yasar da gawar ta a kan gadar Otokutu da ke kusa da hanyar Udu DSC , a karamar hukumar Ughelli ta kudu a jihar Delta. Wannan sai sake zama kamar wani sabon kashedi ga ‘yan mata masu bin mazaje da ba sun ta halin yaya su ke samun kudin su ba.”

  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An tsinci gawar wata mace a kan gada a jihar Delta | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama