An kori 'yansanda 4 daga aiki akan kwacen N50,000 da cin zarafi | isyaku.com

Babban safeton 'yansandan Najeriya Ibrahim Idris ya kori wasu jami'an 'yansanda su hudu wanda aka same su da laifi bayan sun lika zargin karya akan wani matashi kuma sanadin haka suka kwace kudinsa N50,000 ba bisa ka'ida ba.

Hakan ya biyo bayan sanarwa ne da mataimakin kwamishinan 'yansanda bangaren taimako na gaggawa akan harkar cin hanci da rashawa da tabbatar da da'a na hukumar PCRRU  a jihar Ondo ACP. Abayomi Shogunle ya fitar ga manema labarai akan jami'an 'yansandan da ada suke aiki a ofishin 'yansanda a garin Ijebu Ode na jihar Ogun.

'Yansandan da aka kora sun hada da (1) AP. No 122800 Inspr. Mufutau Olaosun, (2) F/No. 366127 Sgt. Adebayo Temitope, (3) F/No. 455593 Cpl. Bakare Taiwo da (4) F/No. 455554 Cpl. Adesoye Ayokunlehin.

An tuhumi korarrun 'yansandan ne a karkashin sashen kundin aikin Dansandan Najeriya na E(3)Gudanar da aiki da bai dace da aikin dansanda ba da kuma sashe na C(2) Cin hanci da rashawa karkashin ka'idar aikin Dansanda na Cap. P19. Dokokin tarayyar Najeriya 2004.

Bayanai sun nuna cewa a ranar 7 ga watan 6 na bana 'yan sandan su hudu suka tare wani matashi wanda ya ciro kudi N50,000 a wani ATM bisa sakon uban gidansa.Bayan ya ciro kudin ne sai kawai 'yansandan suka sha gabansa suka tare shi da motarsu kuma suka tuhumeshi da kasancewa dan yahoo wanda ya musanta lamarin da yasa suka kaishi Ofishin su .

Daga isarsu ofis sai suka tuhume shi da karin wasu laifi da baiji bai gani ba kuma suka tilastashi yayi tsallen kwado kuma suka kwace N50,000 da ya ciro daga ATM.

Bayan da suka sake shi ne ya rubuta sako ta Whatsapp zuwa sashen kula da da'a da harkar cin hanci da rashawa na 'yansanda PCRRU wanda suka fara bincike da yakai ga korar 'yansandan su hudu kuma aka maida masa kudinsa N50,000 da batagarin 'yansandan suka kwace masa da farko.

Ga lambobi da adireshin da zaka iya samun sashen taimako na gaggawa akan harkar da'a da cin hanci da rashawa na 'yansanda a ko ina a Najeriya:

PCRRU is available 24/7 via the following channels; Phone Calls Only: 08057000001, 08057000002 | SMS/WhatsApp Only: 08057000003 | BBM:58A2B5DE | Twitter: @PoliceNG_PCRRU | Facebook: www.facebook.com/PolicePCRRU | Email: complaint@npf.gov.ng OR PolicePCRRU@gmail.com


Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN