• Labaran yau

  July 25, 2017

  An kasheta bayan an tura katon itace ta al'aurar ta

  Mazauna garin Nkumba ta tsakiya a gundumar Wakiso na kasar Uganda sun wayi gari cikin mamaki ganin cewa an gano gawar wata mace tsirara mai suna Rose Nakimuli wanda aka samu an kashe ta kuma aka tura wani babban itace ta al'aurar ta aka yar da aita a wani gonar ayaba a kusa da garin Wakiso.

  Bayanai sun nuna cewa Nakimuli ita ce mace ta uku da aka tsinci gawarsu wanda suka mutu ta wannan yanayin ,domin kwanaki uku da suka gabata an sami gawar wata yarinya 'yar shekara 17 a Wayana ta gabas a mace ita ma tsirara bayan an yi mata fyade.

  Yayin da yake jawabi ga manema labarai a wajen da lamarin ya faru shugaban 'yansanda na gundumar Entebbe Godfrey Ninsiima ya ce an kama mutum 9 da ake zargi da hannu a lamarin.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kasheta bayan an tura katon itace ta al'aurar ta Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama