• Labaran yau

  July 30, 2017

  An kashe basarake aka kona gawarsa

  Yanayin tsaro sai kara tabarbarewa yake kara yi a cikin kasarnan,a kulli yaumin akan tashi ne da koke na yadda aka aikata wani mugun alkaba'in a cikin al'umma gari zuwa gari .Labari ya bayyana na yadda aka kashe wani basaraken gargajiya  Oba Patrick Fasinu a garin Qwo da ke cikin karamar hukumar mulki ta Yawa na jihar Ogun.

  Sunday Punch ta ruwaito cewa basaraken ya halarci wani taron gargajiya ne a garin Ilaro amma a yayin da yake dawowa sai ya biya ya ajiye direbashi shi kuma ya tuko motarsa kirar Camry sai wasu mahara suka tare shi a dokar daji suka fito da shi daga cikin motar suka sassare shi da adda daga bisani suka maida shi cikin motar kana suka banka wa motar wuta da shi basaraken a ciki.

  Wani daga cikin iyalin mamacin ya ce maharan sun tafi da wayar salular basaraken.

  Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda na jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin ya kara da cewa an gano adda da aka yi amfani da shi wajen kisan basaraken kuma tuni aka fara bincike akan lamarin.  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  kShiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe basarake aka kona gawarsa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama