An gudanar da bikin cin naman kare a yankin Yulin da ke China | isyaku.com

An gudanar da wani bikin cin naman kare a birnin Yulin da ke kasar Sin, duk da rahotannin da aka fitar da fari cewa an soke bikin na wa...

An gudanar da wani bikin cin naman kare a birnin Yulin da ke kasar Sin, duk da rahotannin da aka fitar da fari cewa an soke bikin na wannan shekarar. 

An dai saba yin irin wannan bikin ne duk shekara a birnin da ke lardin Guangxi.

A farkon wannan shekarar ne wasu masu fafutuka da ke adawa a Amurka suka yi ikirarin cewa hukumomi sun hana sayar da naman kare.

Haka kuma a ranar 15 ga watan Mayu jami'ai a birnin sun tabbatar da cewa ba a yi wannan haramcin ba.

Ko ana sayar da naman kare har yanzu?

Rahotanni daga Yulin a ranar Laraba sun bayyana cewa an rarrataye karnukan da aka kyafe a shaguna a kasuwar Dongkou mafi girma a birnin.

Haka kuma akwai rahotannin da ke nuna cewa an baza jami'an tsaro a kan tituna.

Wata mai fafutuka a birnin ta shaida wa BBC cewa 'yan sanda sun hana ta shiga kasuwar Dashichang, inda ta yi imanin ana sayar da karnuka masu rai.

A shekarun da suka wuce an dan samu hatsaniya a lokaci da masu fafutukar kawo karshen al'adar suka yi kokarin kwace karnukan da ake shirin yankawa.

A birnin na Yulin ne aka fi samun masu cin naman kare a lardin na Guangxi.

Sai dai hakan bai samu jan hankalin duniya ba, sai a shekaru goma da suka wuce.

Shin cin naman kare yana da aibu?

Duk batun na hana azabtar da dabbobi ne da kuma sauyi kan yadda Sinawa ke kallon karnuka.
Mazauna birnin da kuma masu sayar da naman karen na cewa, suna kashe karukan ne ba tare da sun wahalar da su ba, kuma cin naman ba shi da wani bambanci da cin naman alade ko akuya ko kuma kaza.
An kwashe shekaru ana wannan al'adar ta cin naman kare a kasashen China da Koriya ta Kudu da wasu kasashen da ke yakin Asiya.

Wadanda ke son wannan al'adar ba sa jin dadin abin da suke yi wa kallon katsalandan da baki ke yiwa al'adu na cikin gida.

Cin naman kare a al'adar Sinawa na da amfani a lokacin bazara.

Har wadanda ma ba sa cin naman karen suna kare al'adar, matukar ba sato karnukan aka yi ba, ko kuma an azabtar da su wajen kashe su.

Amma masu suka na cewa ana cunkusa karnuka a cikin keji idan za a kawo su daga wasu birane saboda bikin, kuma ana azaftar da su yayin kashe su.

Masu fafutukar na kuma zargin cewa an sato karnukan ne.

An yi zanga-zanga a ciki da wajen kasar kuma yawan masu ajiye kare a gida ya karu matuka, inda a shekarun baya-bayan nan suka kai miliyan 62.

Kuma hakan na tasiri wajen sauya ra'ayin masu cin kare.

Me ya kawo rudani a bana?

A watan Mayu, wasu masu fafutuka da ke Amurka sun yi ikirarin cewa an haramta sayar da naman kare a bana. Sai dai ba haka batun yake ba.

Amma hukumomin birnin Yulin sun nanata cewa, ba su suka shirya bikin a hukumance ba, saboda haka ba za su haramta shi ba. Cin naman kare dai ba laifi ba ne a China.

Hukumomi a birnin ba su ji dadin yadda kafafen yada labarai ke yayata bikin na bana ba.

A shekarar 2016, sun hana a yanka karnukan a bainar jama'a saboda tunanin cewa za a yi bore.

A bana ma dai ba a yi yankan sosai a bainar jama'a ba, ko da yake ba a kammala bikin ba tukuna.

Masu fafutuka sun kiyasta cewa a wasu shekarun a lokacin bikin ana kashe karnuka da maguna kusan 10,000 kuma a cinye a bikin na kwana goma.Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Daga BBC

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,25,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,39,JAKAR MAGORI,18,LABARI,416,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: An gudanar da bikin cin naman kare a yankin Yulin da ke China | isyaku.com
An gudanar da bikin cin naman kare a yankin Yulin da ke China | isyaku.com
https://2.bp.blogspot.com/-749G0JnPu1g/WVk4G7rYD5I/AAAAAAAAFew/tOf-83KN4ykEopnPRuedOWD6p5wEbqYOACLcBGAs/s320/_96577256_gettyimages-540540988.jpg
https://2.bp.blogspot.com/-749G0JnPu1g/WVk4G7rYD5I/AAAAAAAAFew/tOf-83KN4ykEopnPRuedOWD6p5wEbqYOACLcBGAs/s72-c/_96577256_gettyimages-540540988.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/07/an-gudanar-da-bikin-cin-naman-kare.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/07/an-gudanar-da-bikin-cin-naman-kare.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy