• Labaran yau

  July 31, 2017

  An gano Matsafar kungiyar asiri na Badoo a dajin Lagos

  Rundunar 'yansanda na jihar Lagos ta yi nassarar gano matsafar kungiyar asirri na Badoo (Badoo cult) wadda ta dade tana addaban mazauna birnin Lagos da harkar kashe kashe da tsafe tsafe na tsawon lokaci.

  A shekaran jiya ma rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Badoo ta halaka wani magidanci da iyanlinsa su biyar da dare.

  'Yansanda dai suna iya kokarinsu don ganin cewa sun kawo karshen ayyukan 'yan wannan kungiyar.

  A kwanakin baya mahukunta a birnin Lagos sun nemi jama'a su fallasa duk wanda ake zargi da kasancewa dan  haramtacciyar kungiyar ta Badoo.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An gano Matsafar kungiyar asiri na Badoo a dajin Lagos Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama