• Labaran yau

  July 29, 2017

  Alkali ya yanke hukuncin dauri da bulala 36 a kowane mako akan wasu barayin rogo 2


  Alkalin wata Kotu a garin Abiaja da ke cikin jihar Edo ya bayar da umarnin cewa a dinga yi wa wasu barayi biyu da aka dauresu a gidan kurkuku bulala 36 sau biyu a mako bayan an same su da laifiin satan rogo.

  Hakan ya fito ne daga bakin Cyril Odiboh,wanda lauya ne mai zaman kansa kuma daya daga cikin lauya da ke wakiltar wata kungiyar lauyoyi mai zaman kanta da ake kira Action Aid.

  Cyril Odiboh yace yayi matukar mamaki da wannan irin hukuncin kuma zaiyi bincike domin ya gano ko da Alkalin yayi gaban kansa ne wajen yanke hukuncin ko kuwa haka yake a kundin hukunta laifuka da suka jibanci irin wannan laifin.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Alkali ya yanke hukuncin dauri da bulala 36 a kowane mako akan wasu barayin rogo 2 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama