Yadda albarushi ya ratsa wata karamar yarinya a Maiduguri | isyaku.com

Bayanai sun nuna  cewa an sami rudani a yayin da wasu mazauna anguwannin Jidari da Polo suka yi kokarin samun mafaka yayin da wasu da ake zargin 'yan kungiyar boko haram ne suka kai wani hari a barikin Giwa na soji da ke wajen garin maiduguri inda aka ji karar aman matsakaita da manyan bindigogi da wasu ababen fashewa da misalin karfe 7:00 na yamma a ranar Laraba.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa lamarain ya janyo rudani inda jama'a da yawa mazauna anguwannin da ke kusa da barikin neman mafaka lamarin da yayi sanadin samun kansu a halin da wasu albarussai suka same su ciki har da wata karamar yarinya.

Wata majiya ta shaida mana cewa rundunar soji a Maiduguri sun tabbatar da samun nassara ta hanyar dakile wani hari da aka kai a barikin Giwa da ke Maiduguri.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
Yadda albarushi ya ratsa wata karamar yarinya a Maiduguri | isyaku.com Yadda albarushi ya ratsa wata karamar yarinya a Maiduguri | isyaku.com Reviewed by on June 08, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.