Yadda aka yi wa Fulani kisan kare dangi a Taraba | isyaku.com


Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar a matsayin kisan-kare-dangi.

Babban kwamandan runduna ta uku ta sojan kasar da ke Jos, wanda ya bayyana hakan, ya dora alhakin hakan kan shugabannin kabilar Mambila.

Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya fadi hakan ne a fadar Sarkin Mambila da ke jihar ta Taraba yayin wani taro da shugabannin al'ummomin yankin.

A cewarsa, "An yanka kananan yara 'yan shekara biyu, an kashe mata masu ciki; abin da aka yi musu ya fi abin da 'yan Boko Haram ke yi, domin 'yan Boko Haram ba sa kashe kananan yara. Niyya aka yi ta yi musu kisan-kare-dangi".



Birgediya Janar Ahanotu ya kara da cewa, "Binciken da na yi ya yi yadda ake matukar nuna kiyayya ga Fulani a nan, sannan kuma an yi musu barna sosai; yanzu babu wani dan Fulani a wannan yanki in ban da wadanda suka gudu domin tsira, da kuma wadanda ke zaune a cikin gari. An yi yunkurin share su daga doron kasa ne."

Ya ce har a ranar Litinin jami'an soji sun gano gawarwakin Fulanin da aka kashe, yana mai cewa rundunarsa ta tura karin dakarunta domin tabbatar da zaman lafiya.
Daruruwan mutane ne ake fargabar sun mutu a tashin hankalin ya barke a makon jiya tsakanin Fulani da Mambilawa a karamar hukumar Sardauna.



Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120.DOWNLOAD OUR APPLICATION.APK 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN