• Labaran yau

  June 02, 2017

  Yadda aka bizine safeton dansanda da ransa | isyaku.com

  An gano gawar Safeton dansanda Musa Sunday na sashen manyan laifuka da fashi da makami na SARS wanda ya bace tun watan Nuwambar bara a wani kabari mara zurfi a Ibeju Lekki da ke garin Lagos.

  Bayanai sun nuna cewa an kama Sunday ne aka azabtar da shi kafin aka bizine shi da ransa a bisa umarnin wani basaraken gargajiya.Bayanan kuma sun nuna cewa Sunday yana gadin wani fili ne da ake rigima akansa wanda tuni rigimar tayi sanadin mutuwar wasu mutanen kafin shi Sunday.

  Wata majiya ta labarta mana cewa Sunday yana gadi a wannan filin ne da shi da wasu yansanda su uku ba a bisa ka'ida ba a bisa umarnin na gaba da shi wanda ya sanya sunayen su a jaddawalin gadi ba tare da shaida wa na gaba da shi ba ko Kwamishinan yan sanda na jihar Lagos.

  Sunday ya rasa ransa ne bayan fada ya kaure a filin da suke gadi tsakanin bangarorin da ke rigima akan filin wanda sakamakon hakan yasa daya bangaren suka kama Sunday suka tafi da shi kuma suka azabtar da shi daga bisani a bisa umarnin wani basaraken gargajiya mai suna Baale suka daure hannayensa a baya kuma suka jefashi da ransa  a wani rami suka rufeshi da kasa.

  Bayan shigowar sashen leken asiri na musamman na hukumar yansanda cikin lamarin wanda yasa suka yi amfani da na'urar zamani wajen gano wajen da wayar salular Sunday ta bayar da bayani na karshe akan wajen da yake,rundunnar yansanda na jihar Lagos ta yi amfani da wannan damar inda ta kaddamar da binciken da ya kaita ga gano wajen da aka bizine Sunday da kuma wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

  Yansandan jihar ta Lagos suna tsare da basaraken da ya bayar da umarni a bizine Sunda da ransa da wanda ya daure hannun Sunday kuma ya jefa shi a rami yayin da sauran masu laifi suka arta na kare.

  Safeto Musa Sunday ya mutu ya bar matarsa Halimat yar shekara 27 da yara hudu yan shekaru 4,6,8 da 12 wanda suka shiga wani hali sakamakon rashin jagoran gidansu Sunday.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka bizine safeton dansanda da ransa | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama