• Labaran yau

  June 09, 2017

  Wa'adi: Wasu Igbo sun fara komawa kudu | isyaku.com

  Bayanai da ke shigowa sun nuna cewa wasu 'yan kabilar inyamirai da aka fi sani da suna igbo sun fara ficewa daga Arewacin kasarnan cikin lumana wanda masu fashin baki suke ganin ba zai rasa nasaba da wa'adi da wasu matasa masu kishin Arewa suka bayar ba inda suka bukaci igbo su fice daga Arewa.

  A makon da ya gabata ne wasu matasa suka ba kabilar igbo wa'adin watanni uku su fice daga Arewa,Daily Post ta ruwaito cewa bincikenda tayi ya nuna cewa wasu igbo sun fara komawa garuruwansu inda tashar mota ta  God is Good da ke Mando a Kaduna ta cika makil da 'yan kabilar igbo wadanda ke jiran mota saboda su koma kudu ranar Alhamis.

  Haka kuma tashar Peace Mass da ke Kofar Ruwa a Kano al'umman igbo sun cika a yayin da suke kokarin samun mota domin komawa kudu.

  Duk da yake wasu manya a cikin Gwamnati da kuma al'umma sun yi nuni da cewa duk  dan Najeriya yana da 'yancin zama a duk inda yake so ba tare da wata tsangwama daga kowa ba.  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wa'adi: Wasu Igbo sun fara komawa kudu | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama