• Labaran yau

  June 27, 2017

  Saraki ya soki gwamnatin Najeriya bisa daukaka kara game da wanke shi | isyaku.com

  Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya soki gwamnati bisa daukaka kara game da hukuncin da kotun da’ar ma’aikata ta yanken a wanke shi daga tuhume-tuhumen da ake masa.
  Ya ce, wannan wani yunkuri ne bin duk wata hanya don a durkusar da shi a siyasance.Ofishin yada labara na Saraki ya sanar da cewa, wannan yunkuri ne kawai na sake sabuwar Shari’a a kafafan yada labarai kan Sarakin wanda kuma gwamnatin ba ta da dalilan yin hakan.

  Saraki dai nam ayar da martani ne ga yunkurin daukaka kara da gwamnatin Najeriya ta yi bayan an wanke shi a kotu bisa zargin karya wajen ayyana kadarorin da ya mallaka.
  A ranar 14 ga watan Yuni ne kotun ta wanke Saraki daga zarge-zarge 19 da ta yi masa.  Ku biyo mu a shafin mu na Faceboo @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120.DOWNLOAD OUR APPLICATION.APK 

  Daga TRT 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saraki ya soki gwamnatin Najeriya bisa daukaka kara game da wanke shi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama