• Labaran yau

  June 08, 2017

  Rundunar sojin sama ta Najeriya ta musanta hannu a zargi juyin mulki | isyaku.com

  Rundunar sojin sama ta Najeriya NAF ta musanta zargin cewa wasu jami'anta suna da hannu a cikin zargin yunkurin juyin mulki a makonnin baya.

  Daraktan labarai da hulda da jama'a na rundunar ta kasa  Air Commodore Olatokunbo Adesanya ya shaida  wa manema labarai cewa "zai kasance da mamaki a wannan karni na 21 a sami wadanda zasu yi tunanin kafewa a tsari irin na juyin mulki na soja matsawar yana cikin hayyacin tunani  na gari"

  Olatokumbo ya kara da cewa rundunar sojin sama runduna ce ta kwararrun mutane masu hazaka da ilimin zamani wajen tafiyar da aikin su,kuma rundunar ta dage ne don ganin ta cimma nassara ta fannin tsare darajar Najeriya daga kowace irin barazana.  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rundunar sojin sama ta Najeriya ta musanta hannu a zargi juyin mulki | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama