• Labaran yau

  June 15, 2017

  Mutum 9 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Niamey | isyaku.com

  Mutane 9 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Yamai babban birnin kasar Jamhuriyar Nijar.
  Sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ambaliyar ta afku.

  Ana neman wasu mutane 2 da suka bace sakamakon ambaliyar ruwan.

  Mazauna yankin da lamarin ya faru sun fito waje a tsakar daren jiya tare da kawana a tsaye. Kayan amfanin gidaje sun bi ruwa tare da gudu wa. Haka zalika dabbobi da dama sun mutu.

  A shekarar da ta gabata sakamakon ambaliyar ruwa a Nijar sama da mutane dubu 38 ne suka mutu inda wasu dubu 92 suka samu raunuka.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.


  Daga shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 9 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Niamey | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama