Matsafi ko barawon yaro: Yunkurin sace yaro a garin Ambursa | isyaku.com

A ranar Asabar da ta gabata a garin Ambursa,wani mutum mai suna Hassan ya yaudari wani dan karamin yaro dan shekara 4 inda ya tafi da shi zuwa wani kangon gida da ake ginawa a unguwar sabon garin Ambursa.Ba wanda ya san manufar wannan mutum dangane da yaron mai suna Sulaiman Nasiru Ambursa.Daga inda mutumin ya dauko yaron zuwa kangon gidan kimanin tazarar mita 500 ne wannan ya haifar da shakka akan ko miye manufarsa bayan ya dauko yaron zuwa wannan gidan.

A tattaki da ISYAKU.COM ya yi zuwa garin Ambursa,Mal.Umar Mustapha Muhammed Dan Amo Ambursa wanda ganau ne ba jiyau ba kuma Kawu ga shi yaron ya shaida mana cewa misalin karfe 9:00 na safiyar Assabar aka kira shi aka shaida mashi cewa wani mutum ya dauki Sulaiman zuwa wani gida kuma a yayin da suka isa  wajen sun tarar cewa ya fitar da wasu kayakin shi ko na saddabaru ne ko wani abu makamancin haka.

Wata karamar yarinya ce ta gan lokacin da mutumin ya tafi da Sulaiman sai ta sheka ta gaya wa yayar ta kuma ta nemi agaji daga makwabta,bayan bazuwar labarin aukuwar lamarin sai jama'an gari suka yi dafifi lamarin da ya sa wasu jama'a suka yi yunkurin yanke danyen hukunci akan mutumin amma gayyato jami'an tsaro wanda suka shigo cikin lamarin da gaggawa ya sa ran mutumin ya tsira daga halaka.

Akalla mota biyu ne karin jami'an tsaro na 'yansanda daga Birnin kebbi suka kai dauki saboda dakile yiwuwar daukan danyen hukunci daga jama'a sakamakon da ya sa suma 'yan sandan suka sha da kyar amma babu wanda aka raunata ko jikata sakamakon lamarin.

Mal.Umar ya kara da cewa mutumin yayi kusan kwanaki biyu a garin na Ambursa a yayin da ake ganinsa a wani Masallaci da kur'ani guda biyu da wasu litaffai na Musulunci yanayin da ya sa ba'a zarge she da wata mummunar manufa ba tun farko.

A yayin da yake tofa albarkaci bakinsa game da lamarin Uban kasar Ambursa Alh Muhammadu Wangarawa ya shaida mana samun labarin aukuwar lamarin wanda sanadin haka har ya je Ofishin 'yan sanda a garin Birnin kebbi inda yatarar jami'an 'yansanda suna gudanar da bincike akan lamarin.Ya kuma bukaci jama'an garin Ambursa su dinga kawo rahoto da bincike akan duk wani bako da ba'a sanshi ba ko ake ganin wani take-take da ba'a amince da shi ba.

Bincike da ISYAKU.COM yayi a yau ya nuna cewa rundunar 'yansanda a garin Birnin kebbi ta mika wanda ake tuhumar a sashen kwararru na CIB da ke babban hedikwatar hukumar a Gwadangaji domin kammala bincike da zai kai ga gurfanar da Hassan gaban Kotu.



@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN