MASSOB ta nesanta kanta daga Kanu kan zancen Biafra | isyaku.com

Shugaban Kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra Ralph Uwazurike, ya nesanta kan sa da Nnamdi Kanu da ke neman amfani da tashin hankali a fafutukar sa.

A wata ganawa da ya yi da wasu shugabanin kungiyoyin arewa a Kaduna don ganin an fahimci juna, Uwazurike ya bukaci a samar da zaman lafiya, tare da yin bayani a kan yadda kungiyar MASSOB a karkahin sa ta kwashe shekaru 18 ta na fafutuka ba tare da yamutsi ba.

Uwazurike, ya kuma yi bayani a kan yadda ya kafa gidan Radiyon Biafra, ya kuma sanya Nnamdi Kanu a matsayin darakta, amma ‘yan siyasa su ka yi amfani da shi wajen sauya manufar kafa tashar.

Shugaban ya ce, manufar kafa gidan rediyon ita ce, wayar da kan al’ummar Igbo tare da ilmantar da su, amma aka maida rediyon wani dandalin yada sakonnin kyama da makarkashiya da razana jama’a.

A karshe ya bada tabbacin cewa, babu abin da zai samu ‘yan arewa da ke zama a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Daga shafin Liberty
MASSOB ta nesanta kanta daga Kanu kan zancen Biafra | isyaku.com MASSOB ta nesanta kanta daga Kanu kan zancen Biafra | isyaku.com Reviewed by on June 14, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.