• Labaran yau

  June 08, 2017

  Koriya ta Arewa na ci gaba da nuna wa Amurka yatsa | isyaku.com

  Duk da barazanar takunkumi da yanke huldar jakadancin da manyan kasashen duniya ke yi ga Koriya ta Arewa amma hakan bai sa ta daina gwada harba makamai masu linzami ba.

  Ba a dauki sama da mako guda ba da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya dauki matakin fadada takunkumi ga Koriya ta Arewa sai ga shi kasar ta sake gwada harba makamin.

  Koriya ta Kudu ta sanar da cewa, Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami ta kasa zuwa cikin teku.
  Wannan ne karo na 10 da Koriya ta Arewa ta gwada harba makamin a bana.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


   Koriya ta Arewa na ci gaba da nuna wa Amurka yatsa ya fara bayyana a shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Koriya ta Arewa na ci gaba da nuna wa Amurka yatsa | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama