Ko ya dace a yi gwajin cutar sikila kafin aure? | isyaku.com

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia, mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al'umma baki daya. 

Mun yi rashin kwararru da dama domin wannan larura. Na rasa wani abokina na kut-da-kut mai suna Nura, wanda muka lakaba ma sunan "88 soja" sakamakon wannan cutar. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen wayar da kan jama'a game da illar ciwon sikila. Muna iya dakatar da wannan ciwon. Muna iya hana yaduwarsa.
Kawata Samira Sanusi ta yi fama da wannan ciwon na tsawon fiye da kashi biyu cikin uku na rayuwarta. An yi mata tiyata fiye da sau 10, kuma an sha kwantar da ita a asibiti sabili da matsalolin da sukan biyo bayan jinyar da ciwon na sikila ke haifarwa.

A duk lokacin da na ga wani mai fama da cutar sikila yana kuka saboda radadin cutar, sai na ce dama iyayensa ba su yi son kai ba. Ka ga, abu ne mai sauki kafin mu yi aure mu daure mu yi gwaji daga nan sai mu yanke shawara a kan ko ya kamata mu mu yi auren ko a'a.

ADIKON ZAMANI: Shin ya dace mace ta yi aikin ofis?
Ana gadon cutar sikila ne daga iyaye masu dauke da wasu kwayoyin halitta na jini, wato haemoglobin, masu kamar lauje. An fi samun cutar a tsakanin Larabawa da 'yan asalin nahiyar Afirka.

Kwayoyin halittun jinin na sauyawa (su koma siffar lauje), wanda yake jawo raunata kwayoyin halittar, wanda yakan zama hanyar kamuwa da ciwon amosanin jinin.

Amosanin jinin na janyo daukewar numfashi, da gajiya da jinkiri wajen girman jiki. Yana kuma sa idanu da fatar jiki su sauya zuwa launin ruwan kwai. Duk wadannan alamu ne na amosanin jini.

Ana kamuwa da cutar amosanin jini ne idan aka gaji nau'in wasu kwayoyin halitta (SS) daga iyaye. Idan mutum ya gaji kwayar halittar amosanin jini daga daya daga cikin iyayensa, kana ya gaji kwayar halittar da ba ta da amosanin jini daga daya bangaren, zai kasance mai halittar AS.

Amma hanya mafi kyau wajen dakatar da yaduwar wannan ciwon shi ne idan muka rage auratayya a tsakanin nau'in AS/AS, da AS/SS da SS/SS. Hanyar tabbatar da wannan ita ce ta gwajin jinin masu niyyar yin aure.

Wannan kira ne ga masu niyyar yin aure da su gwada irin 'kwayoyin halittar su, watau genotype, kafin su yi aure.

Kuma kira ne ga iyaye da shugabannin addini da su tabbata an shigar da gwaje-gwajen kafin kowanne daurin aure ya gudana. Kada mu ci gaba da raunata rayuwar 'ya'yanmu da jikokinmu. Jahilci ba dalili ba ne.
Komai yawan soyayyar da kake yi wa masoyiyarka, abin da ya fi kyau shi ne kuje a gwada ku kafin ku yi aure, domin kada soyayyarku ta zama kiyayya. Ka ga kun ceci 'ya'yan da za ku haifa daga rayuwa dake cike da wahala.

Daya daga cikin bakin da suka tattauna a kan wannan batu a ADikon Zamani na rediyo, Alhaji Umar Farouk, ya ce, "Rabuwa da budurwar da na so na aura yana daga cikin muhimman shawarwarin da na taba yankewa a rayuwata".

Yau shi da tsohuwar budurwar tasa sun sami 'ya'ya masu ingantacciyar lafiya bayan da suka auri wadanda suka fi dacewa da su. Lallai akwai darasin sadaukar da kai a cikin wannan labarin.
A je a yi gwajin amosanin jini a yau!



@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


Ko ya dace a yi gwajin cutar sikila kafin aure? ya fara bayyana a shafin BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN