• Labaran yau

  June 23, 2017

  Kisan gilla ga Fulani: Gwamnati tarayya ta aika karin jami'an tsaro zuwa jihar Taraba

  Gwamnatin tarayya ta aika karin jami'an tsaro zuwa jihar Taraba da ke arewa maso-gabashin kasar sakamakon hari da aka kai wa makiyaya tare da kashe su da barnatar da dukiyoyinsu.

  Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.
  Kakakin mkaddashin shugaban Laolu Akande ya sanar da cewa, Osinbajo ya bayar da umarnin tura karin sojoji da sauran jami'an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru domin kare afkuwar wani rikicin.

  Wannan mataki ya biyo bayan Fulani sun aike wa da mukaddashin shugaban Najeriya wasikar cewa, an yi musu kisan kare dangi a Taraba.

  Kafafan yada labarai na yankin sun sanar da cewa, an kashe Fulani kusan 100 a rikicin da aka yi a Taraba. Amma babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da hakan.   @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.


  Daga shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kisan gilla ga Fulani: Gwamnati tarayya ta aika karin jami'an tsaro zuwa jihar Taraba Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama