• Labaran yau

  June 17, 2017

  kawanyar da Al-Shabab ta yi wa Mogadishu yazo karshe | isyaku.com

  Jami’an tsaro sun kawo karshen kawanya ta wanni 10 da ‘yan ta’addar Al-Shabab suka yi wa Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

  Wani jam’in dan sanda Ali Adnan ya shaida wa ‘yan jaridu cewa, ‘yan ta’addar Al-Shabab sun kai dauki kan wani gidan sayar da Pizza bayan kai harin kunar bakin wake a otel din Posh da ke kusa da gurin.

  Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida ta Somaliya Ahmad Muhammad ya ce, jami’ansu sun kawokarshen kawanyar da Al-shabab ta yi wa birnin Mogadishu na tsawon awanni 10.

  Ya kara da cewa, akalla akwai mata 7 da wani dan kasar Siriya 1 da suka jikkata.

  Ya kuma ce, an kubutar da ‘yan kasar Kenya 2 da dan kasar Itopiya daya daga hannun ‘yan ta’addar.
  Kungiyar ta’adda ta Al-Shabab kuma reshen Alqa’eda da ke Somaliya ta dauki alhakin kai hare-haren.  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

  Daga shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: kawanyar da Al-Shabab ta yi wa Mogadishu yazo karshe | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama