• Labaran yau

  June 10, 2017

  Kebbi: Karin canja sheka daga PDP zuwa APC da mika tuta ga yan takara | isyaku.com

  A yau ma an sami wasu karin jama'a da suka canja sheka daga jam'iyar PDP suka koma jam'iyar APC a jihar Kebbi.Da yawa daga cikin jigajigan PDP sun koma APC a yau 10,Yuli,2017 a wani taro na jam'iyar da aka gudanar a filin wasa na Haliru Abdu a cikin garin Birnin kebbi,taron da Gwamnan jihar Sokoto Alh.Aminu  Tambawal ya halarta.

  An mika tutoci na jam'iayar ga wadanda zasuyi takara a karkashin jam'iyar a kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi.

  Taron ya sami halartar tsofaffin jigajigan yan PDP wadanda suka canja  sheka zuwa APC kuma suka yi mubaya'a ga Gwamnan jihar Kebbi da jam'iyar APC.

  Gwamnan jihar Kebbi Alh.Atiku Bagudu a yayin da yake jawabi,yayi godiya ga jama'ar da suka canja sheka daga PDP zuwa APC inda ya nuna cewa "alhairi ne,kuma alhairi baya yawa".

  Ya kuma kara da cewa duk da yake anci karfin adawa a jihar Kebbi amma wajibi ne a kula da ababen da jama'a ke bukata kuma a tabbatar an aiwatar da su idan da hali.

  Alh.Atiku Bagudu ya bukaci a zauna lafiya kuma a fito gaba daya a zabi jam'iyar APC a lokutan zabe.

  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Karin canja sheka daga PDP zuwa APC da mika tuta ga yan takara | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama