Kabilar Igbo a Kebbi: Bama fuskantar wata barazana | isyaku.com

Shugaban kabilar Igbo mazauna jihar Kebbi Mr.Samuel Nnamani yace kabilar Igbo basa fuskantar wata matsala na zamantakewa tsakaninsu da jama'ar jihar Kebbi a ko ta wani fuska..

Mr.Nnamani yana bayani ne a yayin zantawa da ISYAKU.COM akan ko akwai wata barazana da Igbo ke fuskanta sakamakon wa'adi na watanni uku da wasu matasa masu kishin Arewa suka bayar a Kaduna a makon da ya gabata wanda hakan yayi sanadin wasu Igbo sun fara komawa gida a wasu jihohin Arewa .

Shugaba Nnamani yace "babu wani dan kabilar Igbo da ya gudu a cikin jihar Kebbi sakamakon wannan barazanar,ya kara da cewa idan ma har wani ya tafi gida ai saidai tafiya ta kasuwanci ko ganin gida wanda aka saba da shi yau da kullum".

"Marigayi Sarkin Gwandu Haruna Rasheed yayi kyakkyawar tsari ta hulda na lumana a zamantakewa tsakanin kabilar Igbo mazauna jihar Kebbi,bayan rasuwarsa kuwa Sarki Jokolo ya bi ta kan wannan tsarin hakazalika Sarki Iliyasu Bashar na yanzu yana kan wannan tsarin tsakaninsa da Igbo."

Mr Nnamani ya kammala da cewa "Sarkin Musulmi,Sarkin Katsina,Gwamnan Kaduna,Gwamnan Kebbi da kuma da yawa daga cikin manyan mutanen Arewa su yi Allah wadai da wannan barazanar ta matasan.Saboda haka mu Igbo hankalinmu a kwance yake domin ba inda zamuje da ya wuce mu zauna a kasar mu Najeriya mu nemi abinda zamu ci.Da kudu da Arewa ai duka Najeriya ne."



@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN