• Labaran yau

  June 02, 2017

  Jirgin sama mafi girma a duniya na gaf da fara tashi | isyaku.com

  A jihar Kalifoniya ta Amurka an dauki tsawon shekaru 4 ana aikin samar da jirgin sama mafi girma a duniya wanda a yanzu aka fito da shi daga garejin da aka samar da shi a ciki.

  Jirgin mai suna Stratolaunch na da kananan fika-fikai kuma an samar da shi ne don amfanin sojoji.

  Jirgin na da nauyin kilogram dubu 226 kuma zai iya daukar kaya masu nauyin kusan kilogram dubu 250.

  Ana shirin amfani da jirgin samfurin Pegasus don harba makaman roka.

  Bayan an gama gwajin injinan jirgin ana sa ran fara ta shinsa a shekarar 2019.


  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

  Daga shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jirgin sama mafi girma a duniya na gaf da fara tashi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama