• Labaran yau

  June 03, 2017

  jaririn sa da ya zama abin bautawa | isyaku.com

  Wani jaririn sa da aka haifa da kai,kunne,ido da hanci irin na dan Adam ya janyo wasu kauyawa sun fara bauta masa a bisa imani da suka yi cewa jaririn sa din wata alamace ta bayyanar ubangijin su na Hindu Lord Vishnu.

  An haifi jaririn sa din ne ranar Alhamis da ya gabata a  Muzaffarnagar, Uttar Pradesh, a gabashin India bayan bazuwar labarin haifuwar wannan sa nan da nan kauyawa da ke kauyukan da ke kusa da Muzaffarnagar suka fara dafifi domin samun yin bauta ga jaririn sa da aka haifa.

  Bayanai sun nuna cewa jaririn sa din ya mutu bayan 'yan awowi kadan da haifuwarsa,amma duk da haka kauyawan basu daina kwarara zuwa wajen da aka haifi jaririn sa din ba saboda su bauta mashi domin neman dacewa daga ubangijin Hindu Lord Vishnu.


  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: jaririn sa da ya zama abin bautawa | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama