• Labaran yau

  June 05, 2017

  Jami'an NSCDC 600 ke aikin samar da tsaro na musamman a Maiduguri | isyaku.com

  Rundunar tsaro ta NSCDC na jihar Borno ta girka jami'anta 600 domin bayar da kariya a wajajen ibada a fadin Maiduguri wanda ya hada da Masallatai a cikin wannan watan na Ramadan.

  Shugaban rundunar ta jihar Borno Mr.Abrahim Abdllahi ne ya shaida wa wakilin kamfanin dillancin labarai ta Najeriya NAN yayin da yake tattaunawa da su ranar Lahadi.

  Kwamanda Abdullahi yace sintirin ya hada da kwararru daga fanni daban-daban na rundunar wanda ya hada da sahen kula da bama-bamai,sashen kwantar da tarzoma da sashen bincike.

  Ya kuma kara da cewa sintirin har ila yau ya shafi sa ido akan wajajen cinkoson jama'a,kasuwanni,manya-manyan supermaket,tashshin mota da sauransu.  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jami'an NSCDC 600 ke aikin samar da tsaro na musamman a Maiduguri | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama